Feb. 19, 2024
Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya mai da hankali ne kan yadda aka gudanar da gasar Polo a Jahar Filato da ke arewacin Najeriya. A wannan karo, club club din wasan kwallon dawakin da suka fafata a gasar sun fito ne daga jihohin Lagos, Nasarawa, Bauchi, Taraba, Kaduna, Kano, Niger da kuma Katsina. A karshe dai club din Keffi Ponies ta jihar Nasarawa ta lashe gasar a karawar karshe da suka yi da Malconmines daga Filato mai masaukin baki.
Ku latsa alamar suti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......