April 8, 2024
A wannan makon Shirin Duniyar Wasanni ya yi duba ne kan yadda ake tufka da warwara game da tsarin tsaro a lokacin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics da birnin Paris zai karbi bakunci a watan Yulin wannan shekarar.
Shire-shiryen gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta Olympics da birnin Paris na Faransa zai karbi bakunci a watan Yuli mai zuwa sunyi nisa, domin dai rahotanni na nuna cewar an kammala tanadin kusan dukkanin inda za a gudanar da wadannan wasanni.
Sai dai wani hanzari ba guda ba, duk da matakan da kasar ta Faransa ta dauka na tabbatar da tsaron ‘yan wasa da kuma na ‘yan kallo, bayanai na nuna cewar akwai alamun fuskantar barazanar tsaro a lokacin gasar.
Wannan lamari dai ya biyo bayan harin ta’addancin da aka kai birnin Moscow wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 140.
A lokacin wata zantawa da aka yi shugaban Faransa Emmanuel Macron a makon da ya gabata, ya ce babu shakka, akwai yuwuwar Rasha za ta kai hari a lokacin gasar da ke tafe.
Kai hari a yayi gasar gujeguje da tsalle-tsalle ta Olympics a iya cewa ba sabon abu bane, domin a baya an sha samun irin hakan, wanda aka kai a shekarar 1972 a Munich da kuma a shekarar 1996 a Atlanta.
Duk da cewa a cikin watan da ya gabata ministar Wasannin Faransa Amelie Oudea-Castera, ta ce a yanzu babu wata barazanar hare-haren ta’addanci da gasar gujeguje da tsalle-tsalle ta Olympics ke fuskanta, sai dai wasu da dama na cewa barazanar abu ne da ke da alaka da rikicin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine da ya kwashe sama da shekaru biyu anayi, wanda kasashen duniya ciki harda Faransa ke goyonma Ukraine baya domin fafatawa da Rasha.
Ita dai wannan gasa ana ganinta a matsayin wata farfajiya ta samar da hadin kai, ganin yadda take hada dukkanin bangarorin duniya waje guda.
Domin idan aka koma baya cikin tarihi, bayan kawo karshen yakin duniya na biyu, gasar da aka gudanar ta shekarar 1952, ta kasance taron wasanni mafi girma a duniya da aka gudanar.
Ƴan wasa dubu 4 da dari 955 ne suka halarci gasar daga kasashe 69, bayan maido da kasashen Japan da Jamus da wasu kasashe 13 da a karon farko ke nan suka halarci gasar, cikinsu har da Isra’ila wacce ta kasance sabuwar kasar da aka kirkira da ta samu amincewar Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 1948, da Vietnam da ke cikin rudanin siyasa.
To sai dai ana ganin cewa a wannan karon siyasa ta shiga cikin lamarin wanda ke kokarin kawo rarrabuwar kai.
To sai dai a wani martani da Rasha ta maida game da kalaman Macron ta bakin mai magana da yawun fadar shugaban kasar Dmitry Peskov, ta ce zargin na Macron babu tushe a cikinsa kuma wani matakine na yada labaran kanzon kurege da kasashen yammaci ke yiwa Rasha.