June 10, 2024
Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan ci gaban da wasan Damben Gargajiya ke samu a kasar Hausa. Akwai kungiyoyi da dama da a yanzu suka shiga cikin sabgar wasan dambe wanda kuma hakan ke kara mata tagomashi dama jawo ra’ayin wadanda da basa ciki shiga cikinta gadan-gaban. Dambe Warriors na daga cikin kungiyoyi da ke suka jima suna shirya wasan inda 'yan wasan ke samun albashi mai tsoka a mataki daban-daban.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......