July 15, 2024
Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako tare da Khamis Saleh ya mayar da hankali ne kan nasarar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta El-Kanemi Warriors ta lashe kofin kalubale na Najeriya na shekarar 2024.
A karshen watan da ya gabata ne dai ƙungiyar ta Jihar Borno ta samu nasarar lashe kofin kalubale na Najeriya, bayan da doke Abia Warriors da ci 2 - 0 a filin wasa na Mobolaji Johnson da ke Lagos.